Yan bindiga yayan kungiyar Movement for Unity and Jihad in West Africa (MUJWA) guda 9
ne suka halaka a yayinda aka kama wasu daga cikinsu a yakin da ya barke tsakanin yayan wannan kungiyar da mayakan kungiyar buzaye yan tawaye a arewacin kasar Mali.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya nakalto majiyar sojoji da kuma ta kungiyar buzaye yan tawayen National Movement for the Liberation of Azawad (MNLA) suna fadar haka a jiya jumma’a.
Mai magana da yawun kungiyar MNlA Akay Ag Mohamed a garin Kidal, da kuma wasu jami’an sojojin kasar guda biyu, wadanda suka bukaci a sakaye sunanyensu sun ce a kammala fadan a jiya jumma’ amma sun kashe dakarun kungiyar MUJWA 9 a yayin da suka kama wasu daga cikinsu a fadan da suka yi a kusa da birnin Timbuktu a cikin makon da ya gabata.ABNA,
Mayakan kungiyar MUJWA wadanda suke da dangantaka da kungiyar Alka’ida suna daga cikin kungiyar masu riya kishin addini wadanda suka kwace iko da arewacin kasar daga hannun buzyen bayan sun shelante ballewarsu a farkon shekara ta 2012